Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama sama da mutane 30 kan rikicin da ya barke a ranar Litinin a garin Sagamu, wanda ya yi sanadin farmakin akalla rassan banki hudu a yankin Sabo da ke Sagamu da masu zanga-zanga suka yi.
The Nation ta ruwaito cewa, Ita ma Sakatariyar karamar hukumar Sagamu ba ta tsira ba yayin da masu zanga-zangar suka kai hari a ma’aikatunta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ogun Abimbola Oyeyemi, ya ce an dawo da zaman lafiya a garin mai fama da rikici ta hanyar shiga tsakani da kwamishinan ‘yan sanda, Frank Mbah ya jagoranta.
“Komai ya dai-daita a sassan Sagamu yanzu. CP Frank Mba da kansa ne ke jagorantar tawagar ‘yan sanda da wasu sojoji don shawo kan lamarin.
A wani labari kuma, Yadda Na Hana Obasanjo Yin Tazarce — Atiku Ya Yi Bayyani Dalla-Dalla
Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana yadda ya hana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yin tazarce. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Yan takarar yan majalissu a inuwar Jam’iyar da ya gudana a daren ranar Lahadi a Babban birnin Tarayya Abuja.