Al’ummar Kenya a Nairobi babban birnin kasar na gudanar da zanga-zangar lumana kan cin zarafin wata mata da masu tuka babur suka yi.
Wani Faifan Bidiyon da aka yada a yanar Gizo ya nuna yadda ake cin zarafin matar wacce ke Neman dauki daga Al’uma, lamarin da ya dugunzuma hankular mutanen kasar.
Kawo yanzu dai yan sanda kasar sun kame mutane akalla 16 da suke zargi da hannu a faruwar lamarin.
Kazalika kawo yanzu Hukumomi a kasar sun ce, sun kama akalla Matuka Babur sama da 200 da suka karya Dokokin hanya.
Kana masu zanga-zangar karkashin jagoranci kungiyar Fararen hula sun buƙaci ayi Adalci kan cin zarafin matar yar kasar Kenya