By Abbas Yakubu Yaura
Matasa a yankin Gashua da ke jihar Yobe sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kisan wani direba mai suna Mohammed Musa da sojoji suka yi.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a daya daga cikin gidajen mai da ke unguwar Garin Alkali ta hanyar Gashua, hedikwatar karamar hukumar Bade ta jihar.
Hukumomin Sashe na 2 na Operation Hadin Kai da ke Damaturu, da aka tuntube su, sun ce har yanzu ba su samu rahoton faruwar lamarin ba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
Kakakin rundunar shiyyar Laftanar Kennedy Anyanwu, ya yi alkawarin jin ta bakinsa da zarar an samu rahoton lamarin.
Da suke ba da labarin yadda lamarin ya faru, majiyoyi a yankin sun shaidawa gidan talabijin na Channels cewa jami’an soji na cikin sintiri.
An ce sun isa gidan man ne domin aiwatar da dokar hana siyar da man fetur na ‘PMS’ a cikin jarkoki.
“Jami’an soji sun shiga cikin gidan man ne a kan babura da wasu motocin sojoji dauke da kawuna, lamarin da ya haifar da firgici,” in ji Hassan. “Amma sun nemi mutanen da su kwantar da hankalinsu. An harbe wani direba mai firgita da ya yi yunkurin tserewa a nan take.”