Wasu mutane 174 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA), Legas.
Zuwan su na jiya shi ne jirgi na 12 da aka dawo da su ta filin jirgin sama na Legas tare da ‘yan Najeriya kimanin 2,044 sun dawo ne daga Libya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi sabbin ‘yan gudun hijirar da suka iso cikin jirgin Al-Buraq Boeing 737-800, wanda ya sauka da misalin karfe 3:35 na rana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Babban darakta na NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed wanda ya samu wakilcin kodinetan ofishin Legas, Ibrahim Farinloye ya karbi sabbin rukunin tare da sauran jami’an gwamnatin tarayya.
Wadanda aka dawo da su sun hada da manya mata 69, yara mata biyar da jarirai mata 10 yayin da akwai manya maza 75, yara maza 12 da jarirai maza uku.
NEMA ta ce 23 ne suka zo da kananan cututtuka.
Farinloya ya ce, “Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai, sun fara mayar da dubban ‘yan Najeriya da suka makale daga kasashe daban-daban tun daga shekarar 2017 ta hanyar wani shiri na musamman na taimaka wa ‘yan gudun hijira.
“A wannan shekarar kadai, jirgin na yau ya yi jigilar jirgin na 12 a karshen shirin a Legas. Baki daya, kimanin ‘yan Najeriya 2,044 da suka dawo daga kasar Libya, an taimaka musu zuwa kasar ta filin jirgin Murtala Muhammad dake Ikeja.
Daga cikin wadannan, manya maza 848, manya mata 719, yara 180 da jarirai 123 sun kasance adadin 2,044 da aka kawo da su a shekarar 2022.”