Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta cafke mutane 27 da ake zargi barayin man fetur ne a Fatakwal.
Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Talata.
Mista Uwujaren ya ce, an cafke wadanda ake zargin ne, yayin samamen da jami’an hukumar suka kai, a maboyarsu dake Ahoada.
“An kama mutane guda 27 a ranar 10 ga watan Satumba shekarar nan, a karamar hukumar Ahoada, na jihar Rivers, kan zargin su da samun man fetur ba bisa ka’ida ba”
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Mutum ya kashe Direban Keke Napep da duka a Kwara
“An kama su ne a wani samamen da jami’an EFCC suka kai, bayan samun wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zargin mutanen, na fasa bututun mai,” in ji shi.
Mista Uwujaren ya ce, jami’an hukumar EFCC sun kwace dimbin albarkatun man fetur daga hannun wadanda ake zargin, yayin Kai farmakin.
“An kuma kwace jarkoki 20 na man Fetur dake cin lita 25, a hannun wadanda ake zargin.” Inji shi
Ya kara da cewa “An kama wadanda ake zargin ne lokacin da suke kokarin jigilar Man Fetur din, zuwa wurare daban -daban.” a cewar shi.
A wani labarin kuma makamancin wannan
Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC sun mamaye Mitros Residences Annex, wani gidan saukar baki mallakar gwamnatin jihar Ogun da wasu otal guda biyu a Abeokuta tare da cafke mutane 56 da ake zargi da damfara ta kafar sadarwa ta intanet.
Sauran otal-otal din da jami’an hukumar hana almundahana suka mamaye sun hadar da dakunan kwanan dalibai na Daktad dake hanyar Quarry da Cecilia Suites da ke unguwar Ibara a Abeokuta.
Jaridar Dimokuradiyya ta cewa wasu jami’an hukumar ta EFCC sun kai farmaki gidan Mitros Residences Annex da sanyin safiyar ranar Litinin inda suka cafke wasu daga cikin masu masaukin baki da ake zargi da damfara ta kafar intanet.
Jami’an hukumar a yayin samamen sun ce sun kwace wayoyin hannu, da kwamfiyutocin tafi da gidanka da manyan motoci da ake zargin mallakar ‘yan damfara ne.
Daya daga cikin masu masaukin bakin wanda ya zanta da manema labarai , ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake zargi da damfarar sun tsere daga wajen a yayin kai sumamen, yayin da wasu kuma jami’an hukumar ta EFCC suka dauke su.
Kakakin hukumar ta EFCC a ofishin su dake shiyyar Ibadan, Tokunbo Odebiyi, ya tabbatar da faruwar samamen, inda ya ce an cafke mutane 56 da ake zargi a otal -otal daban daban dake Abeokuta.
Mai magana da yawun Rundunar, Wilson Uwujaren, yace an kama wadanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 12 ga Satumba, 2021,sannan ya kara da cewa an cafke wadanda ake zargin a wurare daban daban guda biyu a Benin bayan samun rahotonnin sirri, sannan kakakin yaci gaba da cewa zasu gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
“Abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargi a lokacin da aka kamasu sun hada da motoci guda 13 da suka hada da: Lexus ES 350, Lexus 350, Lexus RX 350, Lexus ES 350, Lexus RX 350, Lexus RX 350, Lexus IS 350, Toyota Venz, Mercedes C300 , Mercedes ML350, Range Rover Evoque, GLK 350 4Matic da Toyota kamri. Sauran abubuwan sune kwamfutocin laptop, wayoyi, takardu da katin shaida, ”inji shi.