Sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma, Smart Adeyemi, ya ce Sanatoci ba za su yi watsi da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ba a yayin da ake ta cece-ku-ce kan zargin cire sassan jikin wani yaro.
Adeyemi ya ce Sanatoci na kokarin ganin yadda za su mara wa Ekweremadu baya duk da zarge-zargen da ake yi masa
Ana zargin Ekweremadu da matarsa, Beatrice da safarar wani yaro zuwa kasar Ingila, domin cire sassan jikin sa
An tuhumi ma’auratan da laifin hada baki don shiryawa da kuma saukaka tafiyar wani, da nufin yin amfani da sassan jikinsa
Wata kotun birnin Landan ta ki amincewa da bayar da belin ma’auratan tare da tsare su duk da cewa ba su aikata laifin da ake zarginsu zasu aikatawa ba.
Sai dai Smart ya ce Sanatoci suna tare da Ekweremadu a halin da yake ciki.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, Adeyemi ya ce, “Wannan batu abin takaici ne. Abu ne da ke damun kowa a Majalisar Dattawa saboda yana cikinmu; amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, na san shi mutum ne mai kima da karfin hali; mutum ne mai kyakkawar ɗabi’a kuma mai matuƙar daraja.
“Amma da ya fadi haka, ina ganin ya yi wuri a fara tunanin ko yana da laifi ko a’a. Dukkanmu abokan aiki ne, muna jin zafi kuma muna tare da Ike Ekweremadu akan wannan. Ba za mu bar shi haka kawai ba.
“Sanatoci da yawa suna ƙoƙari don ganin abin da za mu iya yi ta hanyar ba da tallafi da duk wani tallafi da ake buƙata.
“Amma muna son samun cikakken bayani kan lamarin. Batutuwan dai su ne wanda aka yi saffarar na shi bai kai shekarun da suka dace ba wato 18 ba, don haka ba a iya ganinsa yana da ‘yancin tantance ko zai iya bayar da gabobinsa ga wani mutum na daban.