Kotun Majistare da ke jihar Kano ta bada Umarnin tsare wani matashi dan shekara 17 a gidan gyara hali, a ranar Juma’a bisa zarginsa da fashi da makami.
Matashin wadda ke zaune a karamar hukumar Kura ta jihar Kano, ya na fuskantar tuhume-tuhume guda biyu da suka hadar da na hadin baki wurin aikata ta’addanci da kuma fashi da makami.
Mai gabatar da kara, Asma’u Ado, ta shaidawa kotun cewa, wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yuli a Garin Kura, dake jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani ya zo na daya Cikin Sanatoci 10 Shahararru
Asma’u ta kara da cewa, wanda ake kara da misalin karfe 4.00 na yamma. ya hada baki da wata karamar yarinya ‘yar shekara 17, domin yi wa wata mata Mai suna Aisha Muhammad fashin wayar salula.
Mai gabatar da kara ta kuma yi zargin cewa, su biyun sun caka wa wanda suka kashe wuka a cikin yatsa, sannan suka kwace wayar ta kirar Vivo, wacce ba a bayyana darajar kudin ta ba.
Kazalika ta kuma shaida wa kotun cewa, ita ma karamar yarinyar an so gurfanar da ita a gaban Kotu, amma sai ta mutu yayin da take karbar maganin cutar kwalara a Asibitin Cutar IDH, dake Kano ranar 24 ga watan Agusta.
Asama’u Ado ta kuma ce, laifin ya ci karo da sashi na 97 da 298 na dokar manyan laifuka.
Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifukan da ake zargin sa dashi.
Babban Alkalin Kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya ba da umarnin cewa, a mika fayil din karar zuwa Ofishin Daraktan masu gabatar da kara na gwamnati domin yin nayi binciken da kuma bada shawara.
A karshe Sa’ad-Datti ya dage shari’ar zuwa ranar zuwa ranar 14 ga watan Satumba shekarar 2021 don cigaba da sauraran karar.