Rundunar sojin Nijeriya ta ce wadanda ake zargin cewa sojoji ne wadanda aka kama a cikin wadanda suka yiwa motar banki fashi da makami a garin Abakaliki dake jihar Ebonyi, ba jami’anta bane.
Kanal Aliyu Yusuf, Mataimakin Daraktan yada labarai na runduna ta 82 ta sojojin Nijeriya, shi ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a garin Inugu.
Rundunar sojin ta ce mutum biyun da ake zargin da cewa sojoji ne kuma suna daga cikin wadanda suka yi fashi da makamin ba su daga cikin jami’an rundunar da suke aiki a kowanne sashe na sojin.
Rundunar sojin ta ce yana da kyau al’umma su sani cewa; tun shekarar 2015 da 2018, rundunar sojin Nijeriya ta kore su a aikin soja. Sojoji biyu da aka kama da fashin da makamin sune Kofur Ayeni Samuel da Kofur Emeka Harrison.
Kofur Ayeni Samuel mai lamba 03NA/53/088 an kore shi ne a shekarar 2018 bisa zargin fasa bututun man fetur a lokacin yana bataliya ta 174.
“Korarren Sojan yana Bataliya ta 174 daga makarantar Sakandare ta sojoji, a Ikeja a wani atisayen majalisar dinkin duniya na shekarar 2013. Korarren Kofur Ayeni ya bar wurin aikinsa, inda daga karshe aka kama shi a Ikorodu a jihar Legas a 2018 bisa zargin bisa bututun mai.” Inji rundunar.
Rundunar ta kara da cewa; bisa ga dokokin aikin soja, aka tuhumi Ayeni, inda daga karshe aka kore shi a matsayin Kofur ba Sajent ba.
“Haka shima korarren Kofur Emeka Harrison an tuhume shi, inda aka kori daga ‘7 Division Garrison,’ dake Maiduguri tun a 2015.‘’ inji Yusuf.