An saki Dan wasan gaba na kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United Mason Greenwood bisa cika ka’idojin belj, biyo bayan kwanaki da ya kwashe a hannun yan sanda yana amsa tambayoyi akan zargin da ake yi masa na cin zarafi da kuma yin fyade ga wata budurwa. Kamar yadda rundunar yan sandan Burtaniya ta bayyana a yau Laraba.
An kama Mai shekara 20 din ne a ranar Lahadi, biyo bayan bayyanan wasu hotuna da faifen bidiyo da aka wallafa su a yanar gizo, inda aka ci gaba da tsare shi har zuwa jiya Talata sakamakon zarginsa da cin zarafin budurwar, yi mata fyade, da kuma barazanar kasheta.
Sai dai haryanzu rundunar yan sandan yankin Manchester ba ta fito Karara ta bayyana sunan dan wasan ba, amma ta ce” An saki dan wasa mai shekara 20 din da aka tsare shi tun a ranar Lahadi 30 ga watan Janairun shekarar 2022, bisa zarginsa da aikata fyade, da cin zarafin wata Budurwa, bisa cika ka’idojin beli, amma za a ci gaba da gudanar da bincike.
A lokacin da ya ke tababtar da sakin Dan wasan ga Kamfanin Dillancin Labaran AFP, Kakakin Rundunar yan sandan yankin Manchester ya ce” An sake shi bisa cika ka’idojin beli”