A ranar Alhamis ‘yan sandan jihar Imo suka gurfanar da mutum 72 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar ciki kuwa har da garkuwa da mutane. Kwamishinan ‘yan Sandan jihar, Rabiu Ladodo, a yayin da yake gurfanar da wadanda ake zargin a garin Owerri, ya ce an kama su ne a wurare daban-daban a cikin jihar kasa da mako shida.
Ya kara da cewa; kame bata garin yana da alaka da atisayen “Operation Puff Adder” da Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeirya, ya kaddamar. A cewarsa a yayin atisayensu sun yi nasarar kwato mutum 22 da aka yi garkuwa da su, a yayin da kuma suka kwato ababen hawa 11 a cikin wadannan makwanni. Ya tabbatar da cewa; daga cikin wadanda suka kama akwai jiga-jigan masu garkuwa da kananan yara a gaban iyayensu.
Daga cikin su akwai; Chukwuemeka Onyebuchi, 43, da Aina Nwachukwu , 45, a yayin da ‘yan sandan suka bi sahun kama wadansu kananan yara masu suna Oluwa Chukwu Opanwa ,4, da Promise Opanwa 2. Kwashinan ‘yan Sandan ya ce duka kananan yaran mata ne kuma Iyayensu guda, kuma an sace su ne a Umuobum dake karamar hukumar Ideato South Council a jihar.