Wata babbar kotu a Kano da ke zamanta a kan titin miller road ta bayar da belin shugaban karamar hukumar Fagge, Ibrahim Shehi a kan wata kara da ake zarginsa da laifin karkatar da kudaden da aka samu a cikin gida.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ce ta kai shugaban kara a gaban kotu.
Wanda ake zargin, Ibrahim Shehi ya ki amsa laifuka hudu da ake tuhumar sa da shi a ranar Laraba.
Daga nan ne alkalin kotun mai shari’a Jemilu Shehu Sulaiman ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2022 mai kamawa domin cigaba da sauraron karar.
Karin bayani zai zo a nan gaba