Shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da aka dakatar ta Nijeriya Ibrahim Magu, ya gabatar da takardar korafi ga kwamitin dake binciken zarge-zargen da ake masa kan yadda aka hana shi ganin takardar korafin da aka yi akan sa da kuma yadda kwamitin ke sauraron bahasin shaidu ba tare da an bashi damar yi musu tambayoyi ba.
A wasikar da Lauyansa Wahab Shittu ya rubuta, ya ce tun bayan tsare shi da aka yi ranar 6 ga watan nan, yake gabatar da bukatar ganin korafin da aka yi a kan san na hada baki da azurta kai da amfani da ikon da ya wuce kima akan sa, amma har ya zuwa yanzu bai samu ba.
Rahotanni daga gidan Rediyon Faransa sun bayyana cewa; Shittu ya ce wanda yake karewa har ya zuwa yanzu bai san sharuddan da aka gindayawa kwamitin dake binciken ba da kuma abin da suke bukata, yayin da ya gabatar da korafi kan yadda ake tsare shi a ofishin ‘yan sandan gudanar da bincike ba tare da bayyana masa laifin da ya yi ba da kuma bashi damar kare kansa.
Wasikar ta kuma yi korafi kan yadda aka mayar da shi kamar mai laifi, yayin da kafofin yada labarai ke ci gaba da bata masa suna wajen yada labaran karya game da shi.
Daga cikin irin wadannan labaran, kamar yadda wasikar ta nuna, harda zargin ya baiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo naira biliyan 4 wanda Osinbajo ya musanta da gudanar da wasu asusun ajiya a boye da baiwa wasu na kusa da shi damar tafiyar da wasu harkokinsa da kuma sayen wasu kadarori a Dubai.
Lauyan ya ce wadannan zarge-zarge sun yi matukar illa ga rayuwar wanda suke karewa da kuma ita kan ta Hukumar EFCC.
Shittu ya ce wadannan matakai sun mayar da Magu kamar wani babban mai laifin dake samun suka daga jama’a duk da yadda ya sadaukar da ran sa wajen yiwa kasa aiki a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.