Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu na babban kotun gwamnatin tarayya dake Abuja, a ranar Talata ya yi barazanar korar karar hukumar yaki da rashawa wato EFCC wanda suka shigar kan tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke. Mai shari’ar ya ce zai yi watsi da karar EFCC din ne idan har hukumar suka kasa dawo da Diezani a watan Maris din 2020.
Rahotanni sun bayyana cewa; hukumar EFCC din a ranar 11 ga watan Nuwamban 2018 suka shigar da karar tsohuwar ministar suna zarginta da aikata laifuka goma sha uku, wanda ya hada da almundahana da kudaden kasa.
Har wala yau hukumar na zarginta da dibar kudin da ya kai Dala miliyan 39.7 da kuma wadansu naira biliyan 3.32 wanda ta yi amfani da su wajen siyan wadansu kadarori a Abuja, Legas, Fatakwal da kuma jihar Ribas a yayin da take Ofis.
A yayin da aka sake dawo wa kotun kan shari’ar, Alkali Ojukwu ya yi barazanar watsi da shari’ar idan har hukumar suka kasa gurfanar da tsohuwar ministar a watan Maris din 2020.
Lauyan da ya shigar da karar, Faruk Abdullah, ya roki Alkalin da ya dage shari’ar ba tare da sanya lokaci ba domin a cewar Lauyan EFCC din na fuskantar matsaloli wajen dawo da tsohuwar Ministar daga kasar Birtaniya.
Abdullah ya shaidawa Alkali Ojukwu cewa; duba da yanayin, akwai bukatar Alkalin ya dage shari’ar ba tare da ayyana lokacin dawo wa ba.
Diezani dai na Birtaniyar tun shekarar 2015 bayan barinta Ofis.