Babbar kotu a jihar Filato a ranar Laraba ta dage sauraren shari’ar da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang da sama da fadi da naira biliyan 6.3 da kuma tsohon ma’ajin kudi Yusuf Pam zuwa ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.
EFCC sun fara gurfanar da Jang da Pan ne a cikin watan Yunin 2018, inda suke zarginsu da aikata laifuka 17 ciki kuwa harda almundahana da kudi, da kuma zambo cikin aminci da rashawa.
EFCC sun ce laifukan da ake zarginsu da shi ya sabawa sashe na 315, 309, 19 da kuma 22(5) na dokokin fenal kod da kuma dokokin aikata rashawa na 2004.
Mai Shari’a Christy Dabup na kotu ta IV, ya dage karar ne saboda hutun da gwamnatin tarayya ta bayar na bukukuwan sallah babba.