Yan sanda a kasar Pakistan na tuhumar tsohon Firaministan kasar Imran Khan, da akaita laifukkan dake da nasaba da ta addanci.
Binciken nasu na zuwa ne bayan ya zargi yan sanda da ɓangaren Shari’a a kasar da tsarewa tare da azabtar da makusantansa, Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Tuni dai magoya bayan Khan sukayi dan- dazo a wajen gidan tsohon firaministan, inda sukayi barazanar ta yar da husuma idan aka cigaba da tsare shi.
Yanzu dai an bayar da belin shi sai izuwa ranar Alhamis dinnan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Bayyana Manufofinsa, Idan Aka Zabe Shi Shugaban Kasa
Tun a watan Afrilu wannan shekarar Mista Khan ya kasance mai sukar gwamamnatin Pakistan da rundunar sojin kasar.
Yan sanda dai sun bayyana wadannan zarge zarge ne dai bayan da tsohon firaministan ya zargi mahukunta da gallazawa wani na hannu damansa wanda shima ake binciken sa da laifin ta yar da fitina da nuna kiyyaya ga gwamnati.
Jami’ai ƙasar sun zargi Mr Khan da keta dokar yaki da ta’addanci a kasar da zargin yin barazana ga jami’an tsaron Palistan.
Rahotanni sun nuna cewa, daruruwan magoya bayan tsohon firaministan ne suka taru a kofar gidansa da ke Islamabad bayan bazuwar labarin binciken nasa , inda suka lashi takobin karɓe iko da babban birnin kasar idan ‘yan sanda suka ci-gaba da kokarin tsare shi.
Manyan manyan Abokanan siyasar tsohon firaministan sun bayyana cewa kame Mista Khan tamkar ketare jan layi ne a Pakistan.
Wannan dai na zuwa ne a dai lokacin da dangantaka tsakanin gwamnatin Pakistan da tsohon firaministan da aka a cire daga mulki a wata kuri’ar yankan kauna da aka kada a watan Afirilu ke ƙara zafi tare da ɗaukar wani sabon salo.
Tun a wancan lokaci, tsohon firaministan ya ke ci-gaba da yin maganganu masu tsauri da suka tunzura gwamnatin da kuma sojojin kasar tare da yin kira da a sake yin sabon zabe .
Duk da korar da aka yi masa, Imran Khan na ci gaba da samun goyon bayan yawancin yan ƙasar ta Pakistan.
A watan da ya gabata, jam’iyyarsa ta PTI ta doke abokan hamayyar ta bayan ta karbe iko da wani babban lardin Punjab, inda ta doke jam’iyyar PML-N a wani abu da ake kallo a mastayin babbar nasarar da suka samu cikin cikin sauki.
A WANI LABARIN KUMA: Rasha Ta Zargi Ukraine Da Hannu A Kisan Diyar Makusancin Shugaba Putin
Jami’an tsaron FSB na kasar Rasha sun fada a ranar Litinin din nan cewa, kasar Ukraine ce ke da hannu a harin bam da aka kai a wajen birnin Moscow da ke wajen birnin Moscow, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yar dan rajin ra’ayin rikau Alexander Dugin.
Dugin – mai fafutuka mai tsaurin ra’ayi kuma mai goyon bayan harin Kremlin a Ukraine – ana tunanin shi aka nufa da harin da aka kai.