- Mutanen mu suna kwana ciki tsoro da firgici
- Yara basa iya zuwa makaranta saboda tsoron ɓarayi ƴan ta’adda
- Ɓarayi sun taso Zaria a gaba
Sarkin Zazzau ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan yadda ayyukan ta’addacin ɓarayi ke ƙara ta’azzara a yankin musamman ma dai a cikin yan kwanakin.
Sarkin yace abun wanda babu wanda zaiyi fatan shigowarshi yankin ya riga da ya fara yin yawa, inda ya bayyana cewa yansu mazauna garin Zaria na rayuwa ciki tsoro da kuma shakku saboda ɓarayi da suke neman addabar yankin.
Idan baku manta ba, a ranar alhamis ɗin data gabata ne dai wasu ƴan bindiga suka kai hari a makarantar Nuhu Bamalli dake cikin garin Zaria inda suka kashe ɗalibi ɗaya tarr da yin awon gaba da wasu mutane goma ciki hada lakcarori guda biyu.
Karanta wannan: ISWAP ta saki ma’aikacin jin ƙai tare da wasu mutum tara

Jaridar The nation wallafa cewa a wani sabon harin da aka kai ranar Lahadin nan data gabata a rukunin wasu sabbin gidaje dake ƙofar kona duk a cikin birnin na Zaria, an tabbatar da sace mutane aƙalla goma sha biyu bayan da ɓarayi suka farmaki yankin.
Sarkin a yayin da yake jawabi a lokacin da kwamitin tsaro na jihar ƙarƙashin jagorancin kwamishnan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya kawo mishi ziyara, ya bayyana cewa yaransu yanzu basa iya zuwa makaranta saboda tsoron faɗawa hannun ƴan ta’addan dake kara kaina a ko ina.
Kwamishnan yace sunzo ne domin su jajantama sarkin na Zazzau kan waɗannan hare-hare na ƴan ta’adda da suka addabi yankin.
Ya bama sarkin tabbacin cewa yanzu haka an jibge jami’an tsaro isassu a ƙanan hukumomi guda sha biyu dake ƙarƙashin masauratar ta Zazzau.
Sai dai Aruwan yace ba dole bane ace jami’an tsaro zasu iya shiga duka lunguna da saƙo na faɗin lardin, a don haka suna buƙatar haɗin kan masarautun gargajiya.