Wata kungiya mai zaman kanta ta bada tallafin lafiya kyauta wa mata da marayu sama da dari biyar a birnin tarayya Abuja.
Shugaban Kungiyar Mista Samson Ocholi ya ce kungiyar ts dauki matakin hakan ne don kara inganta harkar lafiya da gwamnati ke yi wa al’umma.
Kazalika ya ce an zabo zaurawa wadanda mazajen nasu ne da kuma Marayu bisa irin yadda suka fi galabaita tsakanin al’umma.
Ya kara da cewa Ƙungiyar tare da hadin gwiwar karin wasu kungiyoyi masu zaman kansu za ta ci gaba da bada kulawar lafiya kyauta ga wadanda suka amfanar indai wani ciwo ya kama su.
Wani jami’in lafiya a Ƙungiyar Dakta Chidi Umeokoli ya ce hakika wannan dama ce da mata da marayun za su baiwa kansu kulawa ta musamman a kowane lokaci.