By Abbas Yakubu Yaura
Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya, a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa ma’aikatan lafiya 20 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa tun daga farkon shekarar nan, yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 48.
Cibiyar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na baya-bayan nan game da cutar zazzabin Lassa, wanda aka buga a shafinta na intanet.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa zazzabin Lassa, cuta ce da ke yaduwa a Najeriya, tana faruwa a duk shekara amma ana samun karuwar kamuwa da cutar a lokacin rani.
NCDC ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su “ci gaba da kasancewa da yawan zargin cutar zazzabin Lassa, su yi taka tsantsan tare da lura da alamun zazzabin Lassa. Ba duk zazzaɓi ba ne maleriya.”
Tun bayan bullar cutar ta karshe a shekarar 2016, NCDC ta lura cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar. A shekarar 2019, cibiyar ta lura cewa an samu rahoton bullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da jimillar mutane 1,165 a yayin da cutar ta yi kamari.
Sannan NCDC ta kuma tabbatar da jimillar mutane 4,632 da ake zargi da kamuwa da cutar a shekarar 2021.
Binciken rahoton halin da ake ciki na baya-bayan nan ya nuna cewa an samu rahoton mutuwar mutane 48 da ma’aikatan lafiya 20 da suka kamu da cutar a sabuwar barkewar cutar a fadin kasar.
Cibiyar ta kuma bayyana cewa an samu rahoton mutane 513 da ake zargin sun kamu da cutar inda 66 aka tabbatar da su a dakin gwaje-gwaje.
NCDC ta ce, “Yawancin wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun karu idan aka kwatanta da wanda aka bayar a daidai wannan lokacin a shekarar 2021.
“A cikin dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 75 cikin 100 sun fito ne daga jihohin Edo da Bauchi da kuma Ondo.
“Mafi yawan rukunin shekarun da abin ya shafa na tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne.
“Jahohin da NCDC ta bayyana wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Benue, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Plateau, Cross River, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun, Kwara, Legas, Delta, Gombe, FCT, Nasarawa, Rivers da kuma jihar Enugu.
“Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya tana kuma aiwatar da shirin yaki da cutar zazzabin Lassa a jihohi masu nauyi.”
Ya kara da cewa, “Zazzabin Lassa yana farawa ne kamar kowanne irin zazzabi kamar zazzabin cizon sauro. Alamominsa sun hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon makogwaro, raunin jiki gaba daya, tari, tashin zuciya, amai, gudawa, ciwon tsoka, ciwon kirji, sannan a lokuta masu tsanani, zubar jinin da ba za’a iya bayyanawa ba daga kunnuwa, idanu, hanci, baki da sauran kafofin budewar jiki.
“Lokacin da ke tsakanin kamuwa da cutar da bayyanar alamun cutar kwanaki uku zuwa 21 ne. Magani da wuri da ganewar asali yana ƙara damar rayuwa. “