By Abbas Yakubu Yaura
Bayanai daga cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya a ranar Asabar sun nuna cewa akalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon zazzabin Lassa a cikin makonni uku.
Wannan dai ya zo ne kamar yadda cibiyar ta bayyana cewa an samu rahoton bullar cutar guda 759 a cikin wannan lokaci a fadin jihohi 26 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Tun bayan bullar cutar ta karshe a shekarar 2016, NCDC ta lura cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar. A shekarar 2019, cibiyar ta ce an samu bullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da adadin mutane 1,165 da suka kamu da cutar a kololuwar annobar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da fara daukar matakin gaggawa kan cutar. Hukumar NCDC ta ce aikin ya zama dole ganin yadda aka samu karuwar masu dauke da cutar zazzabin Lassa a fadin kasar nan.
Rahoton halin da ake ciki na baya-bayan nan ya nuna cewa mutane 72 a halin yanzu suna kan jinya, 369 kuma ana bin su, yayin da ma’aikatan lafiya hudu suka kamu da cutar a shekarar 2022.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Benue, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Ebonyi, Plateau, Cross River, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun, Kwara, Lagos, Delta, Gombe , FCT, Nasarawa, Rivers da kuma jihar Enugu.
Cibiyar ta lura da cewa, “Lokacin da ke tsakanin kamuwa da cutar da bayyanar alamun cutar shine kwanaki uku zuwa 21. Magani da wuri da ganewar asali yana ƙara damar rayuwa. “
Rahoton ya kara da cewa, “Zazzabin Lassa yana farawa ne kamar kowace irin zazzabi kamar zazzabin cizon sauro. Alamominsa sun hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon makogwaro, raunin jiki gaba daya, tari, tashin zuciya, amai, gudawa, ciwon tsoka, ciwon kirji, sannan a lokuta masu tsanani na zubar jini da ba za a iya bayyana shi ba daga kunnuwa, idanu, hanci, baki da sauran Kafofin budewar jiki.