Cutar zazzabin Lassa ta yi sanadin mutuwar mutane 40 a watan Janairu, kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce.
A cikin rahoton halin da ake ciki a ranar Lahadin da ta gabata, cibiyar ta ce mutuwar mutane 40 na wakiltar adadin masu mutuwa (CFR) da kashi 19.0 cikin 100 kasa da wadanda suka suka mutu a daidai wannan lokacin a shekarar 2021 wanda ya kai kashi 22.2 cikin dari.
Rahoton ya kuma nuna cewa an samu mutane 211 da aka tabbatar sun kamu da cutar daga cikin jimillar mutane 981 da ake zargin sun kamu da cutar. NCDC ta ce a cikin jimillar jihohi 14 sun samu akalla mutum guda da aka tabbatar a kananan hukumomi 43.
“A cikin dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 82 cikin 100 sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo da Bauchi.
Cibiyar ta ce babu wani sabon ma’aikacin lafiya da lamarin ya shafa a mako na hudu na watan Janairu.
Kana NCDC ta ce: “An bude cibiyar hadin gwiwar zazzabin Lassa ta kasa, Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta sassa da yawa (EOC) don daidaita ayyukan mayar da martani a dukkan matakai.”