Tsohon Dan Wasan Arsenal da a yanzu haka ke fafata Wasa a Ƙungiyar Fernaberhcé na Kasar Turkiyya Mesut Ozil ya a sake yin wani Zazzafar Kalamai dangane da Kisan kiyashi da ake yi wa al’ummar musulmi na Kabilar Uighur dake Ƙasar Myanmar.
A wani sako da wallafa a shafin sa na Instagram a sanyin safiyar yau Juma’a, Ɗan wasan ya ce lallai ko wane musulmi na kwarai ba zai ji daɗin abinda ke faruwa da al’ummar Rohingya ba.
Dan wasan ya ce ya kamata a zauna guri guda a rayuwa kamar mutane ba dabbobi ba domin ta hakan ne za a mori zaman duniya.
Kazalika ya ce addu’a ga al’ummar ta Rohingya ga Musulmi na da matukar muhimmanci la’akari da irin halin kisan kiyashi da ake yi musu.
Idan za a iya tuna dai a baya Ozil ya yi kwatankwacin wanan magana kan abinda ke faruwa a kasar, lamarin da ya kai ga kasar China da ake zargi da wannan aika-aika ta dakatar da sanya dan wasan a cikin wasan kwallo na na’urar Kwamfuta wato PES.
Kazalika wannan lamari ya haifar da rudani tsakanin sa da kungiyar sa ta Arsenal a wanchan lokacin, wanda ake ganin haka ne yayi sanadiyar ajiye shi a benchi da ta kai ga ya yi bankwana da kungiyar.
A hannu guda ma kalaman nashi sun janyo mishi hasarar kudaden shiga na talla da yake yi wa kamfanin buga kayayyaki na adidas bayan da ya ƙi janye kalaman nashi kamar yadda kamfanin ya bukata.