Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, yana son ‘yan wasan Los Blancos Karim Benzema da Ferland Mendy su hadu da shi a Paris Saint-Germain idan ya zama kocinsu na gaba.
Ana ci gaba da alakanta Zidane da aikin horar da PSG.
KU KARANTA: Har Yanzu Malamai 300 Ba Su Karbi Albashin Su Ba a Kaduna – NUT
Hasashe ya karu kan makomar kocinta Christophe Galtier a PSG bayan da kungiyarsa ta gaza.
PSG ta sha kashi uku a jere, ciki har da rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 1-0 a gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA a kwanaki 16 da suka gabata.
Zidane ya dade yana zama babban mafarkin ga PSG, wanda take burin ganin sun koma tafiya tare.
Sai dai a cewar El Nacional, idan tsohon kocin na Real Madrid zai karbi aikin, yana son Benzema da Mendy su bi shi zuwa Parc des Princes.
A wani labarin kuma: Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa yake tausayawa talakawa akan canjin kuɗi
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙasa a inuwar Jam’iyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce tushensa a matsayin ɗa ga ƴar kasuwa ne ya bashi damar fahimtar matsalar da canjin kudi ya kawowa a tsakanin al’umma.
Wannan na Ƙunshe ne a cikin wata sanarwar Ofishin Watsa Labarai na Tinubu Abdulaziz Abdulaziz ya fitar a ranar 17 ga watan Fabrairu na Shekarar 2023.