Najeriya da Portugal sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin gwiwa a bangarori daban-daban kamar shawarwarin siyasa; Ci gaban Mata da Yan Mata, da sauransu.
an sanya sannu kan yarjejeniyar ne yayin wani taro da suka gudanar tsakanin manyan kasar Portugal da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yau juma’a a birnin Lisbon.
A cewar wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban Najeriyar na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta ce yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ta hada da shawarwarin siyasa; Koyarwar Diflomasiya, Bincike da Musayar Bayanai; Haɗin kai a Fannin Al’adu; da Hadin kai a Fannin Ci gaban Mata da ‘Yan Mata.
Sauran sun haɗar da Karfafawa da Al’amuran Jinsi; Matasa; da Wasanni.
Sanarwar mai taken ‘Nigeria, Portugal sun sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama a bangarori daban-daban.’
A cewar Shehu, jami’an majalisar ministocin kasashen biyu ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a wani bangare na ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kai kasar Tarayyar Turai.
A wani taron kasuwanci da aka shirya a yayin ziyarar, inda aka kammala wasu daga cikin yerjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumomin inganta zuba jari da cibiyoyin kasuwanci na kasashen biyu, shugaba Buhari ya bayyana irin ci gaban da aka samu wajen rattaba hannu kan yarjejeniyoyin a matsayin kyakkyawan ginshiki na habaka kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Buhari da firaministan kasar Portugal, Antonio Costa ne suka halarci bikin rattaba hannun.