Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Juma’ar nan, ya umarci hukumar raya birane ta jihar da ta gaggauta bude shedikwatar jam’iyyar (NNPP) ta Maiduguri da aka garkame.
Daily trust ta ruwaito yadda hukumar ta rufe shedikwatar NNPP a ranar Alhamis tare da cafke wani dan takarar Sanata na jam’iyyar.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, gwamnan ya bayyana matakin a matsayin “lokacin da bai dace ba”.
Sai dai mai magana da yawun gwamnan ya ce da zarar Gwamnan ya fahimci matakin da hukumar ta dauka, ya ba da umarnin a sauya shi.
Karanta kuma: Jami’an Tsaro Sun Garkame Shedikwatar Jam’iyyar NNPP
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Al’ummar Jihar Borno nagari suna sane da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata Hukumar Raya Birane ta Jihar Borno tana gudanar da gyare-gyare da suka hada da rufe wasu gine-ginen da wasu mutane ke gudanar da su, da hukumomi kamar Bankuna da ma ma’aikatu wasu cibiyoyi na gwamnati da ke fitar da dokokin da suka saba wa dokokin da suka shafi rashin bin ka’idojin tsare-tsare na garin Maiduguri.
“Duk da cewa hukumar ta yi ikirarin cewa ta yi hakan ne a kan wasu ofisoshi, ta hanyar rufe shedikwatar NNPP bisa kuskure da nufin canza wurin zaman ofishin, Gwamna Zulum na kallon matakin da hukumar ta dauka a matsayin kuskuren lokaci.
“Zulum ya yi imanin cewa, ko da akwaihujja, hukuncin da hukumar ta yanke ya zama dole a ba shi fassarar siyasa wanda zai iya zafafa siyasa da haifar da rudani mara amfani.
“Saboda haka, tuni Gwamna Zulum ya ba da umarnin cewa hukumar ta dakatar da nata dokar kan wannan aiki na rufe ofishin NNPP. Gwamnan ya yi imanin cewa soke hukuncin yana cikin maslahar al’umma gaba daya domin samun zaman lafiya.
“Gwamna Zulum ya yi imanin cewa ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa su kasance masu ‘yancin gudanar da ayyukansu bisa ka’ida, kuma ‘yan kasa su kasance masu ‘yancin yin cudanya da jam’iyyun siyasar da suka ga dama ba tare da wani shamaki ba.
“Zulum ya kuma shawarci hukumomin da ke tunkarar al’amuran da za su shafi jam’iyyun siyasa da su yi la’akari da bukatar gayyatar masu ruwa da tsaki na dukkan jam’iyyun da ake da su domin tuntubar juna da kuma yin hadin gwiwa a kan ayyukan da suka dace da dokokin jihar da ake da su ba tare da tauye ‘yanci da dukkan jam’iyyun siyasa a jihar Borno”
A wani labarin kuma: Na Fita Daga NNPP — Shekarau Ya Zargi Kwankwaso Da Wulakantashi
Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP, duk da cewa bai fito karara ya bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
Shekarau a lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa, a ranar Litinin a ofishin gidauniyar Kano da ke kan titin BUK, ya zargi tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da cewa ba wai kawai ya ci amanar sa ba ne, har ma ya wulakanta shi.