By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya nada Bala Isa a matsayin sabon babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno.
Mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan hulda da jama’a Isa Gusau shine Wanda ya bayyana hakan acikin wata sanarwa daya fitar ranar Litinin a Maiduguri,sannan kafin nadin Isa ya kasance malami a jami’ar jihar Borno.
Isa wanda ya kasance dan shekara hamsin ya fito ne daga karamar hukumar Bayo ta jihar Borno.sannan “Ya kuma kasance Babban Malami a Kwalejin Ilimi ta Kashim Ibrahim, dake Maiduguri.
“Isa, a halin yanzu yana kammala karatun digirinsa na uku a Jami’ar Maiduguri, inda yayi M.Sc.a fannin ilimin sinadarai, da kuma B.Sc. a dai wannan fanni, duka daga Jami’ar ta Maiduguri.
Sannan “Ya kuma yi Difloma a fannin Ilimi daga kwakejin ilimi ta Kashim Ibrahim dake Maiduguri.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Ya yi karatunsa na Sakandare a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Biu, da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kwaya Kusar.