Zulum yace Talauci na iya Tilastawa Ƴan gudun Hijira shiga Ta’addanci
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana fargabar cewa tabarbarewar arziki da talauci idan ba a magance ba, na iya tilastawa wasu ƴan gudun hijira shiga kungiyar Boko Haram da kungiyar mayakan IS da ke yammacin Afirka (ISWAP).
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Ministan Buhari ya buƙaci Kotu ta haramtawa Tinubu, Atiku Takarar Shugabancin Ƙasa
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a jiya a yayin rufe sansanin ƴan Gudun Hijira na Dalori-1, Dalori-2, Gubio da Muna da ke Maiduguri, ya ce Gwamnatin jihar ba za ta iya ci gaba da ajiye mutanenta a sansanonin ƴan gudun hijirar ba.
Ya ce Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an maida mutane matsugunnin su cikin mutunci.
Zulum ya ce: “Hanya daya tilo da za a magance matsalolin ‘yan tada kayar baya ita ce Gwamnati ta magance tushen abin da ya hada da ƙaruwar talauci, ktarancin ababen more rayuwa da kuma yanayin da ake ciki.
“Saboda haka, abin da ya kamata mu yi shi ne mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa gidajen su cikin mutunci. Babu wanda aka tilasta wa komawa gidan shi, muna nan don tallafa kamar yadda yarjejeniyar Kampala take.
“Za a tallafa wa jama’a da abin dogaro da kai domin su samu abin dogaro da kansu idan ba haka ba mutanenmu za su ci gaba da zama a sansanonin ‘yan gudun hijira,” inji shi.
Gwamnan ya ce za a rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira kafin cikar wa’adinsa yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bullo da wani tsari mai ɗorewa da matsakaici don daƙile dogaro da tallafin jin kai da ‘yan gudun hijirar ke yi.
Zulum ya yaba wa shugaban Asusun Tallafawa wadanda abin ya shafa Janar Theophilus Danjuma (rtd) da kuma gidauniyar bayar da tallafi, ga wadanda abin ya shafa da Gwamnatin jihar cikin sama da shekaru 13.
Ya kuma bukaci wadanda suka dawo da su yi amfani da tallafin da kyau tare da tallafawa ƙoƙarin Gwamnati na sake tsugunar da su ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani.