Gwamnan Jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana aniyarsa bayan kammala wa’adin mulkinsa a 2023, yake cewa zai koma taimakon alumma don karshen shi tazama da sauki.Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Gwamna Masari ya bayyana hakane lokacin da yake gabatar da wata kungiya dake tallafawa matasa mai suna Aminu Bello Masari Youth Empowerment Foundation, AMAYEF, da aka gudanar a Jahar Katsina.
Masari yake cewa “Duba da karshen wa’adin mulki na na zuwa a shekarar 2023, na zabi na mayar da karshen aikin gwamnati na ya zama abun tunawa, ta hanyar zakulo matasa zarata da marasa karfi ina tallafa masu wadanda ke cikin yanki na. Wannan shine manufar kafa wannan kungiyar.”
KARANTA:- An yi dauki badadi bayan Yan bindiga sun sake farmakan wani yanki a Abuja
“Duba da matasa sune kashin bayan kowace al’umma, sune keda damar sauya akalar tafiyar kasar nan a nan gaba musamman cikin wannan lokaci mawuyaci da muke ciki.”
“Yanayin tallafin da akewa matasa shine ke bada damar samun nagartattu a cikinsu, don cigaban al’umma.”
“Shi yasanya na zabi na samar da wannan kungiyar mai tallafawa matasa, mai suna Aminu Bello Masari Youth Empowerment Foundation, AMAYEF,.” Kamar yadda gwamnan ya fada.
Aminu Bello Masari yayi kira ga masu hannu da shuni dake cikin al’umma dasu tallafawa matasa, Mata, marasa karfi, marayu, da sauran jama’a domin su samu dogaro da kansu.
Karanta:- Emile Smith Rowe ya sabunta kwantiragin shi da Arsenal
A lokacin da ake kaddamar da kungiyar, an rabawa gajiyayyu kujeru 200 da aka samo daga kananan hukumomi 34 dake Jahar Katsina.
Alhaji Kabir Mashi, shugaban kungiyar ta Aminu Bello Masari Youth Empowerment Foundation, AMAYEF, yace kungiyar ta samu sunayen matasa da marasa karfi da gajiyayyu domin cigaba da tallafa masu.
Yace daga cikin ayyukan kungiyar za ta cigaba da rabawa al’umma Magunguna kyauta, gami da koyar dasu sana’oi daban-daban.
Daga cikin gajiyayyu da suka sami kayan tallafin, sun nuna godiyarsu ga gwamna Aminu Bello Masari, sannan sunyi kira ga masu hannu da shuni dasu shigo a cigaba da tallawa matasa don samun dogaro dakai.