Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce karkashin sabuwar alaka tsakanin kasar da Rasha, sabbin makamashi za su shiga Nijeriyar bisa alkawurran da za su fadada tsohuwar dangantar kasashen biyu ta fuskar kimiyya kasuwanci da kuma makamashi.
Cikin wata sanarwar gwamnatin Nijeriya bayan taron da shugabannin Afrika fiye da 40 ke halarta a Rasha, ta ruwaito Muhammadu Buhari na cewa taron zai farfado da alakar kasar da tsohuwar tarayyar Soviet.
Muhammadu Buhari, ya ce bisa yarjejeniyar da suka kulla da Rasha bangarorin biyu za su yi cudanya tare da amfanar da juna ta fuskar Cinikayya Kimiyya al’adu da kuma ilimi.
Taron na kasashen Nahiyar Afrika da Rasha irinsa na farko karkashin jagorancin shugaba Vladimir Putin, Muhammadu Buhari ya ce Rasha tsohuwar abokiyar Nijeriya ce tun a lokacin yakin basasa ta yadda ta tallafa matuka wajen tabbatar da wanzuwar Najeriya kasa guda dunkulalliya.
A shekarun 1960 dai Rashan ta taimaka a Nijeriya ta bangarorin da suka shafi Ilimi albarkatun karkashin kasa da tsaro baya tamakawa wajen bunkasa kasar.
Sai dai a wannan karon Muhammadu Buhari ya ce alakar Nijeriya da Rasha za ta fi mayar da hankali wajen bunkasa albarkatun man fetur da iskar gas da kuma taimakon Soji musamman a yaki da Boko Haram.
Cikin kalaman Muhammadu Buhari ya ce abin farin ciki sake dawowar alakar ta Najeriya da Rasha wadda su ke fatan kowanne bangare ya amfana.