Shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump, wanda ya rasa goyon baya a kokarinsa na kalubalantar zababben shugaban Amurka, Joe Biden, ya fito karara yana bayyana muradinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe na gaba.
A yayin da yake jawabi ga bakin da suka halarci liyafar Kirsimati da aka shirya a fadar White House, Trump ya bayyana fatansa na sake ganin su a shekaru 4 masu zuwa.
Duk da cewa ba a bai wa ‘yan jarida damar shiga zauren liyafar da ta samu halartar kusoshin jam’iyyar Republican da dama ba, bidiyon jawabin shugaban mai barin gado ya samu kai wa ga al’umma.