Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana Tamburawa dake karamar hukumar Dawakin Kudu a matsayin wurin da zai kasance yankin masana’antun iskar gas, karkashin aikin shimfida bututu daga Ajaokuta zuwa Kano da ya wuce zuwa Kaduna, na kamfanin man fetur na kasa NNPC.

Kwamishinan yada labaran Jihar Mallam Muhammad Garba shine ya ayyana haka yayi tattaunawarsa da mane labarai, inda ya ce hakan ya biyo bayan taron mako-mako ne da majalisar zartaswar jihar ta yi.

Ya ce kuma baya ga nan tuni aka amince wa gwamnatin jihar da ta gudanar da ayyukan dashen bututan iskar gas a nan yankin na Tamburawa dake kusa da inda ake aikin samar da ruwa na Challawa.

Mallam Garba ya kara da cewa a yanzu haka an umarci hukumar kididdigar filaye da ta hada hannu da kwamitin don samar da kundin da za a tsara ayyukan.

Har wa yau Kwamishinan ya shaida cewa, baya ga wadannan dumbin ayyuka gwamnatin ta kuma bada kwangilar ayyukan hanyoyin masana’antu na jihar wanda kudinsu ya tasan ma naira miliyan 393, 237, 697. 00.

Ya ce wannan aiki zai taimaka matuka wajen inganta tattalin arzikin jihar duba da kusancinsa da inda ake aikin samar da hanyar jiragen ruwa na Dala.

Welcome Back!

Login to your account below

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.