Tarzoma ya sake barkewa a kasar Amurka a yayin da wani dan sanda ya sake harbe bakin fata a kasar. Wanda hakan ya sanya jama’a da dama suka fito tituna suna Allah-wadai da wariyar launin fata da ake nuna musu.
Ƴan sandan kwantar ta tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar a wata unguwa da ke Minneapolis bayan da wani dan sanda ya harbe wani bakar fata.
Lamarin ya faru ne a Brooklyn Center kuma an bayyana sunan bakar fatar da Daunte Wright mai shekara 20.
Hankali jama’a da dama ya tashi sosai yayin shari’ar tsohon dan sanda a Minneapolis Derek Chauvin wanda ake zargi da kisan George Floyd wanda mutuwarsa ta janyo fushin jama’a da gangamin yaki da wariyar launin fata.