By Ishaq Dabai
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban taro na 2 na musamman na hukumar shugabannin kasashe da gwamnatoci na ECOWAS kan yanayin siyasa a Jamhuriyar Guinea.
Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana hakan da safiyar yau Alhamis.
Amakon da ya gabata Osinbajo ya halarci babban taron ECOWAS na ban mamaki kan duba halin siyasar kasashen Guinea da Mali, inda aka gudanar da taron a ranar 8 ga Satumba.
Taron wanda a yanzu haka yake gudana a yau Alhamis zai sake nazarin halin da ake ciki a Kasar Guinea dangane da rahoton babban taron ECOWAS zuwa Conakry.
Mataimakin shugaban kasar, wanda zai bar Abuja da safiyar yau, zai kasance tare da karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu sannan kuma ana sa ran zai dawo Abuja daga baya a ranar Alhamis.