Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce shirye shirye sun kammala domin hada hannu da kasar Denmark domin zuba hannu jari wajen sarrafa abubuwan da aka gama amfani da su.
Gwamna Ganduje Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan Kamfanin Danish Consul a Najeriya, lokacin da suka ziyarci gwamnan a gidan gwamnatin jiha.
Bayanin hakan na kumshe ne cikin wata sanarwa da mai jami’in hulda jama’a na Ma’aikatar Muhalli Sunusi Kofar Naisa ya rabawa manema labarai a yammacin Laraba.
Manufar samar da kamfanin sarrafa ababan da suka gama amfani na a matsayin wani bangaren na kokarin gwamnan wajen habaka bangaren tattalin arzikin jihar.
Kamfanin dai zai dinga sarrafa ababan irin su Shara wajen mayar da ita zuwa Taki na zamani da sauran su.
Gwamnan ya kuma bayyanar shigowar bangarori masu zaman kansu, domin zuba hannun jari, wanda hakan zai taimaka wajen samun kaiwa ga ci.
Abada bangaren jami’in kamfanin Mr Per Christense ya ce a shirye suke domin aiki da gwamnatin Kano, kuma zasu duba yiwuwar hada hannu da Kamfanin Cape Gate wajen cigaba da aiki tare.