‘Yan sanda sun kama wani dan shekara 65 mai suna Sulaiman Rauf, saboda zargin da ake yi na yi wa yarinya fyade mai shekaru 10 a garin Ilase a yankin Idiroko na Jihar Ogun.
Kakakin ‘yan sanda a jihar, Abimbola Oyeyemi, a ranar Alhamis ya shaidawa manema labarai cewa, sun samu nasarar kama mutumin da aka tuhuma amma kuma ya mussanta zargin.
Ya ce” mahaifin ya shaidawa hedikwatar Idi-Iroko cewa mautumin da ya aikata wannan abin yana zaune a unguwarsu ,to a lokacin labari ya iske mu cewa an gansa da yarmu a cikin daki.
“Lokacin da yarinyar ta fito daga cikin dakin da ak zargi a nan ne yayi lalata da ita, sai ta sanar da mahaifinta abin da mai gadin ya yi mata.
“Bayan rahoto, kungiyar DPO Idi-Iroko, CSP Aloko Amodu, ta hanzarta bayani game da sabbin masu bincike ga No. 7 Araromi Street, Ilase inda ake zargi da zama kuma an kama shi da sauri.”