By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya fitaccen likitan fitsari a fannin kiwon lafiya a Kano, Dakta Ibrahim Datti Ahmed.
Shugaban kasar, a cikin karramawar marigayi Dakta kuma dan siyasa wanda ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa, ya bayyana shi a matsayin mutum mai dimbin basira.
“Dakta Datti ya kasance kan gaba wajen samar da kiwon lafiya ga talakawa da mabukata.sannan shugaban yace ba za a manta da koyarwarsa da gudummawar daya bayar wajen kyautata rayuwar al’umma ba. Za a rika tunawa da shi da irin kyakkyawar hidimar da ya yi wa al’umma,” in ji shugaba Buhari a wata sanarwa daya fitar ranar Alhamis ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu.
Shugaban yace al’ummar kasar na tare da iyalan marigayin, da Masarautar Kano da kuma gwamnati da al’ummar jihar Kano a yayin da suke jajantawa likitan, dan siyasa da shugaban addini.
Sanarwar ta ce, marigayi Dakta Ahmed, wanda abokin marigayi shugaban kasa Janar Murtala Mohammed ne, shi ne ya kafa asibitin tunawa da Asmau, wanda a yanzu aka canza masa suna Abubakar Imam Urology Center dake Kano, kuma ya rike mukamin Shugaban Majalisar Shari’a ta Najeriya. .