Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bada shawarar cewa dazuzzuka a Arewa, ƙone su ya kamata ayi domin taimakawa wajen yaƙi da ƴan ta’adda.
A cewar sa hakan zai taimaka wajen ƙarar da ƴan bindiga daɗi, a tattaunawar da yayi da gidan talabijin na Arise TV a ranar Litinin.
Ya kuma yi kiran zuba hannun jari a ɓangaren ma’aikata, kayan aiki, da kayayyakin sojoji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar UBEC Ta Zargi Jihohi Da Gazawa Wajen Bayar Da Tallafin Karatu Matakin Farko
Gwamnan yace “waɗannan ƴan ta’addan na gudanar da aikin su na ta’addanci, sabudda wajen ɓoyewar su daji ne. Shine babbar matsalar. Jami’an tsaro na yin bakin ƙoƙarin su domin gano su.
“Abinda ke gaskiya shine bamu da abubuwan da ake bukata domin magance matsalolin tsaro, a yayinda take cigaba da fantsama, domin babu wani ɓangare na Najeriya da bashi da irin wannan matsalar ba.
“A kowane lokaci nayi amanna cewa, zamu iya ƙone daji gaba ɗaya. Akwai dai ɓarna, amma yafi a share su gaba ɗaya, domin al’ummar mu su dawo noma.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya tace matsalar tsaro shine abinda yafi kawo tsaiko a Shekarar 2021.