Sojoji a Ƙasar Burkina Faso sun sanar a gidan Talabijin na Jahar a ranar Litinin cewa, sun karɓe Mulki a wata ƙasa a yammacin Afirka ta Yamma, tare da korar dukkanin Muƙarraban Gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan da suka sanya bazan ɓata lokaci wajen sanya hannu domin kashe wanda ya hallaka Hanifa — inji Ganduje
Sun kuma bayyana cewa, sun kulle iyakokin ƙasar, tare da shan alwashin “maido da mulki a lokacin da ya kamata.
A ƴan shekarun nan dai sojoji sun karɓi iko da kasashen Afirka da dama , daga farar hula, inda suka fara da Ƙasar Mali.