By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Oyo, ‘Seyi Makinde, ya yi ta’aziyya ga Sanata mai wakiltar Oyo ta tsakiya, Teslim Folarin, bisa rasuwar matarsa, Angela Nwaka Folarin.
Gwamnan wanda ya bayyana marigayiyar kuma lauya mai koyi, ya bayyana rasuwar ta a matsayin rashi mai ban tausayi.
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Sanatan da ya rasa mai dakinsa, Yekeen Olaniyi, a wata sanarwa da ya fitar ya ce Misis Teslim ta rasu ne a kasar Birtaniya a ranar Juma’a da rana.
Ya ce tana cikin hankalin ta kafin ta rasu.
Sannan ya kara da cewa, “Tare da mika wuya ga yardar Allah Madaukakin Sarki, muna sanar da rasuwar uwargidanmu, mahaifiyarmu da ‘yar uwarmu, Cif (Barista.) Angela Nwaka Folarin.
“An tabbatar da mutuwar matar Sanatan Oyo ta tsakiya a ranar Juma’a da rana wanda numfasa ta na ƙarshe ya kasance a kasar Birtaniya.”