Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da tsare-tsare na nazari da daidaita shekarun ritaya ga malamai daga watan Janairun 2022 tare da wani kwamitin da zai rubuta takardu don aiwatar da aikin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Muhammed Garba, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa, aikin zai bukaci karin albashi da sauran kudaden alawus-alawus na malaman da ba a tanadarwa a kasafin kudin 2021 ba.
Ta kara da cewa, duk da cewa ba a tanadarwa kasafin kudin ba, akwai bukatar a ba da damar fara sabuwar manufar ta fara aiki daga watan jiya.
Garba ya kuma ce, an ba wa kwamitin damar Samar da dalilin da su dace don aiwatar da shirin na bunkasa fannin ilimi a fadin jihar ta Kano.
A cewarsa, kwamitin zai kuma duba tsari da yanayin hidimar malamai domin daukar sabon shekarun ritaya.
Sanarwar ta Kuma yi nuni da cewa, shekarun ritayar malamai za su ƙaru daga shekarun hidima 35 da shekaru 60 zuwa shekaru 40 na hidima da kuma shekaru 65 na haihuwa.