Gwamnatin tarayya ta haramta sayen amfanin gona kai tsaye da ga manoma ‘yan asalin kasar nan da ‘yan kasashen waje kan yi.
Sabuwar dokar wadda ita ce tabbatar da cewa manoman Najeriya gwamnati ta damu da su, a yanzu ta umarci duk wani dan kasar waje da ya bi ta hannun masu saye na cikin gida masu lasisi don yin kasuwanci da manoma.
Ministan ciniki da saka hannun jari, Niyi Adebayo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na yau Laraba wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi la’akari da hanyoyin da suka dace don tabbatar da farashin kayayyakin masarufi na ’yan asalin Najaria, a wani yunkuri na kare su da kuma tabbatar da cin moriyarsu da kuma tabbatar da cewa sun samu abubuwan da suka dace don ba da tabbacin ci gaba da shiga kasuwancinsu.
Adebayo ya ce ya gabatar da takardu guda biyu a madadin ma’aikatar sa; daya daga ciki shi ne na bunkasa harkar noma a Najeriya ta hanyar farashin kofar gonaki da ya dace da kuma haramtawa ‘yan kasashen waje da wakilansu sayen kayayyakin amfanin gona a kofar gona.
Ya ci gaba da cewa, “A karshe mun samu amincewa daga majalisar zartarwar ta kasa, a yau kan masu saye na cikin gida kawai masu lasisi wadanda dole ne kungiyoyin da abin ya shafa na kasa su yi rajista, su ne za su iya siyan kaya kai tsaye daga hannun manoma su sayar wa ‘yan kasashen waje. Ta haka ne ma manoman ba za su daina yaudarar waɗannan baƙin da kawai suke jefa musu kuɗi su sayi kayansu ba.”