Yanzu Jam’iyyar mu ta APC za ta Ƙara zuwa wani Ƙololuwar Mataki na Cigaba — Inji Sanata Uba Sani
Ɗan takarar Gwamnan Jahar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana gamsuwar sa da yadda aka gudanar da Babban Taron Jam’iyyar APC na Ƙasa, yana mai cewa yanzu Jam’iyyar zata je wani mataki na gaba.
Sanata Uba Sani Ya bayyana haka a lokacin da yake taya murna ga Sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Sanata Adamu Abdullahi, jim kaɗan bayan ya samu nasarar zama shugaban Jam’iyyar.
Dan takarar Gwamnan jihar kaduna Sanata Uba sani a dandalin Eagles Square da ke Abuja, wurin babban taron jam’iyyar APC na kasa.
Sanata Uba ne a lokacin da yake kaskantar da kai tare da musabaha ga sabon shugaban jam’iyyar APC ta kasa mai girma Sanata Abdullahi Adamu.
Sanata tare da sabon mataimakin shugaban jam’iyar na shiyyar (Arewa), Sanata Abubakar Kyari da Sanata Sabi Abdullahi.
Sanata Uba sani tare da Kuma Mai gidan sa Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙaruwar Farashin Dizal: Blue BRT Zasu Tafi Yajin Aikin Na Kwanaki 3
Haka Zalika Sanatan Uba sani ya Taya sabbin zaɓaɓɓun Shuwagabannin Jam’iyyar murnar samun nasara, yana mai ƙara nuna jindaɗin sa ga Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Abubakar Kyari murna a matsayin su na Shuwagabanni.
” Muna alfahari da ku tabbas ku sani Kuna tare da cikakken goyon bayanmu, yayin da kuka daidaita kan aikin daukar babbar jam’iyyarmu zuwa ga mataki na gaba mai girma” Inji Sanata Uba Sani