By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da tsaro.
Ya fadi haka ne a lokacin da yake taya al’ummar musulmi murnar shiga sabon watan Ramadan.
Ya ce, “Ina taya daukacin ‘yan Najeriya musamman al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadan.
“Ramadan wata ne da al’ummar Musulmi a duk fadin duniya suke kiyaye daya daga cikin rukunan addini guda biyar, suke rabawa makwabta da kuma nuna kauna ga duk mutanen da ke kewaye da su.
“Lokaci ne na tunani na ruhi, kamewa, sadaukarwa da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki.
“Watan Ramadan mai alfarma yana ba wa muminai damar tattaunawa da Allah, da rayuwa kamar yadda Annabawansa suka umarce mu da aikata yayin da muke neman albarkarSa da rahamarSa.
“Dalilin wannan lokacin ya fi muhimmanci a gare mu yayin da muke neman mafita da kuma shiryarwar Ubangiji daga kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu a cikin al’ummarmu.
“Gwamnatin Najeriya tana yin duk mai yiwuwa don ganin an daidaita lamarin kuma ta fahimci cewa sai an kara yin komai.
“Majalisar dokokin kasa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na inganta shugabanci na gari domin tsaro, zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
“Ga ‘yan uwa Musulmi, mu yi amfani da damar watan Ramadan wajen yi wa Najeriya addu’a, mu sani cewa Allah yana karbar addu’o’in masu imani.”