By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi barazanar kawo sojojin haya daga kasashen waje domin yakar ‘yan ta’addan da ke yin katsalandan a dazuzzukan jihar Kaduna idan gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza magance ta’addancin.
DUBA WANNAN LABARIN: Ramadan: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bukaci ‘Yan Najeriya Da Suyi Addu’ar Samun Zaman Lafiya Da Tsaro
El-Rufai, wanda ya zanta da ‘yan jarida jim kadan bayan bayyana wa shugaban kasa kashe-kashen da aka yi a jihar Kaduna da suka hada da harin bam da aka kai ranar Litinin a layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar mutane tara tare da sace wasu mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba. Gwamnoni ba za su da wani abin da ya wuce daukar matakin kare rayuka da dukiyoyin al’ummarsu.
Da yake magana da yaren Hausa, El-Rufai ya ce: “Na kai karar shugaban kasa, kuma na rantse da Allah, idan ba a dauki mataki ba, mu gwamnoni za mu dauki matakin kare rayukan al’ummarmu.
“Idan yana nufin dauko sojojin haya na kasashen waje su zo su yi aikin, za mu yi hakan ne don magance wadannan kalubale.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a shekarar 2015 ne aka zargi gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da daukar hayar sojojin daga Afirka ta Kudu domin yakar Boko Haram duk da cewa gwamnatin tarayya ta lokacin ta musanta wannan ikirarin.
Sai dai El-Rufai wanda ya ce shugaban kasar ya tabbatar masa da cewa za a dauki matakin kawo karshen ta’addanci nan da ‘yan watanni masu zuwa, ya bayyana cewa hanya mafi dacewa da za a magance ta’addanci sau da kafa ita ce sojojin Najeriya su yi ruwan bama-bamai a dajin da guraren da ‘yan ta’adda ke tsugune.
Da yake magana kan harin da aka kai a ranar Litinin a layin dogo, ya ce: “Sun zo a shirye kuma sun dade suna shiri kuma sun san lokacin da za su kai hari, na sace VIP.
“Kuma na dade ina cewa dazuzzukan da wadannan ‘yan fashin ke buya, lokaci ya yi da za mu je can mu jefa bama-bamai a kashe duk wadanda ke cikin dajin.
Sai dai idan ba a yi haka ba, wannan matsalar za ta dore kuma tana iya ruguza Najeriya baki daya.
“Wadannan mutane (’yan ta’adda) suna samun kudi. Yadda suke da karfin gwiwa; suna tsoron babu hukuma, babu soja kuma me ya sa jami’an tsaro ba za su je yankunansu su kashe su duka ba?
“Mun san inda suke, SSS na bada rahoto a kowace rana, suna da adadinsu ciki har da na Dogo Gide da abin da yake shirin yi ,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana karara cewa gwamnatin sa ba za ta biya kudin fansa ba domin kwato fasinjojin da aka sace duk da cewa har yanzu ‘yan ta’addan ba su da wata bukata ta musamman.
Ya ce, “Sun tuntubi wasu iyalai amma ba su yi takamaimai wata bukata ba tukuna.
“Ba masu garkuwa da mutane ba ne, ‘yan Boko Haram ne da suka hada baki da ‘yan bindiga suka kaddamar da harin, don haka tunaninmu shi ne, za su bukaci gwamnati ta biya kudin fansa.”
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen zakulo ‘yan fashin tare da kubutar da fasinjojin, yana mai cewa gwamnati za ta ba da fifiko wajen kare rayukan ‘yan kasa kan komai.