By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta gurfanar da wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifuka ciki har da wata matar aure da tayi garkuwa da wani yaro dan shekara uku wanda ya kasance dan makwabcinta ne a Gidan Madi da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato.
DUBA WANNAN LABARIN: Da Katacciyar ‘Yar Majalisar Dokokin Imo Ta Koka Kan Albashin Ta Da Alawus Alawus Da Aka Rike Mata
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato,ASP Sanusi Abubakar, ya ce an kama wadda ake zargin ne a lokacin da ta zo karbar kudin fansa naira miliyan biyu da ta nema daga wajen mahaifin yaron.
Ya ce wadda ake zargin ta bayyana cewa ta samu labarin yadda ake yin garkuwa da mutane ta hanyar sauraron shirye-shiryen rediyo inda ake ba da labarin yadda ake sace mutane.
Mista Abubakar ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ta ajiye yarinyar da aka yi garkuwa da ita a hannun dan uwanta da sunan cewa wanda lamarin ya shafa din dan uwar gidanta ne da ta tafi wani kauye domin samun maganin wata cuta da ba a bayyana ba.
Ya ce daga baya wadda ake zargin ta yi amfani da muryar tsafi wajen canja launin maganarta a wayarta don sanar da mahaifin yaron cewa suna tsare dashi kuma rashin biyan kudin fansa naira miliyan biyu zai sa a kashe yaron.
Ana ci gaba da karbar kudin fansa naira miliyan biyu ne tawagar ‘yan sandan ta kama wadda ake zargin tare da mika ta zuwa hedikwatar ‘yan sandan jihar Sakkwato domin ci gaba da bincike.
Haka kuma an kama wasu barayin guda biyu da aka kama da laifin yin fashi a wani sashe a asibitin kwararru na jihar tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da na’urorin sanyaya iska guda hudu.
Daga baya an kama mutanen biyu da kayayyakin da aka sace kuma rundunar ‘yan sandan ta ce za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike.