By Abbas Yakubu Yaura
Gabanin gudanar da zabukan 2023 da ake sa ran za a yi, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP na iya rasa nasabarta idan har ta kasa lashe zaben shugaban kasa.
Wike wanda ya bayyana aniyarsa ta ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa mai zuwa ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya gana da masu ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyar a jihar Anambra a ranar Asabar.
Hotuna Da Jerin Sunayen Mata 11 Na Marigayi Sarkin Oyo, Oba Lamidi, Daya Mutu Ya Bari
Gwamnan ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su yi watsi da ra’ayinsu tare da yin duk mai yiwuwa domin jam’iyyar ta dawo mulki a 2023.
Ya ce ya yi yaki kuma ya yi nasara a kan jam’iyyar APC mai mulki, inda ya tabbatar da cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasa.
Ya ce, “Ban aiko muku da kowa ba, domin ina girmama ku. Tun daga shekarar 2015 muke jam’iyyar adawa idan ba mu ci zaben nan a 2023 ba, mu ma za mu iya mantawa da jam’iyyar PDP a rayuwar mu.
Wike ya cigaba da cewa don samun nasara dole ne a yi komai domin samun nasarar wannan zabe.
“Ba za a kawo wani tunani ba, kuma duk masu son tsayawa takara, ko mutumin ya fito daga Anambra, Sokoto, Imo, duba mu duka da kyau, wa zai iya tinkarar APC a zaben nan? ni ne.”
Comments 1