Zaɓen Ekiti: Ku guji saida Ƙuri’un ku — Wani Lauya yayi kira Al’umma
Gabanin Zaben Gwamnan Jahar Ekiti, wani Fitaccen Lauya Morakinyo Ogele ya shawarci masu kaɗa ƙuri’a dasu guji saida ƙuri’un su ga Ƴan Siyasa a ranar Zaɓe.
Ya yi zargin cewa Jam’iyya mai Mulki ta APC tana shirin shigo da sayen ƙuri’u, sai yayi kira ga mutanen Jahar dasu guji hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: JAMB ta gargaɗi Manyan Makarantu kan canjawa Ɗalibai Kwasa-kwasan da suka cike
Yace Jam’iyyar ta gaza kwata-kwata musamman ga Al’ummar Jahar a shekarun ta 4 da suka gabata, kuma bata kamata ta cigaba da kasancewa a Mulki ba.
Lauyan yayi zargin ne a cikin wata budaɗɗiyar takarda ga Al’ummar Jahar Ekiti. Takardar dai an tura ta ga Manema labaru a Akure, Babban Birnin Jahar Ondo a ranar Litinin mai taken “Takarda ga Al’ummar Ekiti.
A cewar sa, Gwamnati mai ci a yanzu ta lalata Jahar, sai ya yi kira ga Al’umma dasu kori APC daga Mulki.
Takardar tace “muna kallo a tsanake muga mike fili a Jahar Ekiti, da yanda ta lalata Jahar. Ba wulaƙanci bane kace Gwamnati a Ekiti bata yi komai ba, wajen gina mulkin ta.
Comments 1