Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba harkokin Karatu zai dawo, saboda irin ƙudirin Gwamnatin na shawo kan matsalolin da suka shafi Ƙungiyoyi.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i, da Ƙungiyoyin Manyan Ma’aikatan Jami’a a halin yanzu suna gudanar da yajin aiki.
Da yake jawabi ga Taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa Abuja, Ministan Ƙwadago Sanata Chris Ngige yace ƙarshen yajin aiki yazo.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU za ta janye yajin aikin nan ba da dadewa ba—– Ngige
Ministan wanda ya musan ta zargin Gwamnatin Tarayya na ƙirƙirar wasu manhajoji na biyan Albashi ga Ƙungiyoyin, yace Gwamnati ta gayyaci Hukumomin da lamarin ya shafa ciki har da NITDA, domin tayi bayani akan nasarar da aka samu akan abinda ya sanya Ƙungiyoyin suka shiga Yajin Aiki.
Ngige, a lokacin da yake jawabi yace Gwamnati tana da ra’ayi na ganin Ɗalibai sun koma Makaranta.
Ya bayyana cewa taron ranar Alhamis, yana da manufar duba nasarar da aka samu ciki har da kula da rikicin Albashi na Manhajar UTAS da ƙungiyar ta Ƙirƙira da NITDA ke kula dashi a matsayin
Da sauran manhajoji na U3PS da SSANU da NASU suka ƙirkira.
Ministan yace yana jiran Kwamiti daya ƙunshi Ministan Ilmi, da Shugaban Ma’aikata, dana Albashi da Alawus-Alawus, da Hukumar Kula da Jami’o’i.