Rundunar Ƴan Sanda a Zamfara ta tseratar da mutane 14 da aka sace
Rundunar ƴan sandan Jahar Zamfara ta ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 42 a dajin Kunchin Kalgo da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jahar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau a yau Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kai Tsohuwar Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi gidan yari mai tsanani
Shehu ya ce an samu nasarar kuɓutar da waɗanda harin ya rutsa da su ne a wani samame da jami’an leƙen asiri suka gudanar a dajin a ranar Talata.
Ya ce Rundunar Ƴan sanda ta gudanar da aikin tare da goyon bayan wasu mutane da ke haɗa kai da Jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a jihar.
“Rundunar ƴan sandan ta ɗauki matakin ne da sahihan bayanan sirri akan sun kai farmaki kan Maɓoyar ƴan bindigar, tare da yin nasarar ceto mutane 14 da suka haɗa da jarirai biyu ƴan shekara ɗaya kowanne.
“Waɗanda abin ya shafa sun sanar da ƴan sanda cewa ƴan bindigar sun kai farmaki kauyukan Nasarawar-Wanke da Rijiya a Ƙaramar hukumar Gusau inda suka yi garkuwa da su har tsawon kwanaki 42,” inji shi.
Shehu ya ƙara da cewa an miƙa mutanen 14 ga ƴan uwansu.
Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Ayuba Elkanah ya yaba da goyon bayan da gwamnati da jama’a ke baiwa ƴan sanda a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jahar.
Comments 1