Abokin Takara: Akwai rashin lissafi, da rashin shirin Zaɓe ga APC — Inji Okowa
Abokin Takarar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP Ifeanyi Okowa yace Jam’iyyar APC da Dan Takarar ta basu da wayau.
Okowa yace matsayar Tinubu na tsaida Kabiru Masari a matsayin Abokin Takara manuniya ce na APC Bata wayau da shiri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Ta’adda sun kori wani Sansani mai Sojoji 80 a Borno, sun gudu da Makaman su
Da ake zantawa dashi a gidan Talabijin na Channels a cikin shirin Siyasar mu a Yau, Gwamnan Jahar Delta, yace ɗaukar Masari a matsayin Abokin Takara ya nuna cewa APC Bata da tsari, kuma bata shirya zaɓe ba.
A cewar Okowa “yanzu APC abun ya zame mata wahala ta samo wanda zai yi mata Mataimakin Takara, muna jin abinda bamu taɓa ji ba, wanda aka sanya da farko za’a canja shi da wani.
“Wannan ya nuna akwai rashin wayau, wanda ya sanya muka yarda cewa basu shirya wa zaɓe ba, akwai rikicin lissafi, ba kamar mu ba, tun daga rana ta farko, muka yanke hukunci akan abinda ya kamata muyi.
Comments 1