Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tayi nasara a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers, a gasar Firimiya mai daraja ta daya ta kasa Najeriya.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Rabi’u Ali ne ya fara saka kwallon a ragar Rangers, a mintina na 51, bayan da aka samu bugun Fanareti.
Wasan dai an fafata shi ne a jihar Kano, a Filin wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar mata, wanda kuma wannan wasan shine mako na 35.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/sojoji-dss-yan-sanda-sun-tarwatsa-sansanonin-ipob-a-jihohin-anambra-enugu-sun-kwato-makamai/
Da yake ganawa da manema labarai jim kadan da kammala wasan, Ibrahim Musa ya bayyana jin dadin sa dangane da yadda yan wasan Kano Pillars din suka yi abinda ya kamata, wajen samun wannan nasara.
Ya kuma kara da cewa kungiyar zata sake kimtsawa musamman a wasan da zata buga a waje, inda zasu kara da Nassarawa United da kuma Rivers United.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tana mataki na 13 a teburin gasar, inda take da maki 43 a wasanni 35 da ta buga.